01
Wasikar gabatar da soyayya ga macen da kake matukar jin nauyinta.
Sallama da fatan budewar kofofin farinciki da nishadi a gareki, tare da farinciki mai kima da daraja ga diyar girma da daraja a wajena.
Boyayyen sirri ne zan bayyana gareki, saboda nazarin danayi da kuma shawarwarin dana samu akanki.
Dukkan bishiyoyi da tsuntsaye tare da ruwan sama, duk Allah ya haliccesu ne don su zama jin dadi ga rayuwar dan adam.
numfashi da lafiya duk ba'a sayensu saboda sun zama dole ga rayuwa, haka itama soyayyar gaskiya ba'a sayen ta baiwace daga Allah.
Yanzu idan na sanar dake cewa kindauki kaso mafi tsoka wajen sanyani farinciki ya zakiji?
Aduk sanda muka hadu koda ahanya ne kwarjininki kan bugi zuciyata, tayadda ban iya hada idanuna da naki.
Dayawa sai inji murmushi ya cike fuskata aduk lokacinda nake tunoki, meyasa hakan?
Nidai nasan akullum ina yaban halayenki, musamman sanin girman mutane da kulawa, amma idan nace ayanzu haka sunanki ne nafi yayi da yawan ambato azuciyata ya xakiji?
Ki sanardani maganin damuwata ma'ana ki mallamakamin zuciyarki, hakan kadai zai kawo waraka gareni.
Ko a yanxu nayi riba tunda na mallaka miki tawa zuciyar.
Hakika tun lokacin da idanuna Su kalle ki zuciya ta kamu da ciwon sonki, na aiko miki wannan sako ne ba don komai ba sai don na rasa irin hanyar da ya dace na biyo kwana da kwanaki ina tunani da irin hanyar da zan biyo ta sanar da ke wannan cutar da Allah ya yi min jarabawa da ita, amma ina, na kasa na yi tunanin samun ki a makaranta domin na sanar da ke irin kaunar ki da ke kunshe a cikin zuciyata, sai naga ba mafi sauki irin rubuta miki wannan wasikar.
Ka da na cikaki da surutu ya ke hasken zuciya ta kin riga kin zama ginshikin rayuwata, ina sonki, ina kuma kaunarki, a kullun ke ce abin tunani na, zan rasa dukkanin farin ciki idan har ban samu amincewar ki ba, hakika zuciyata zata dan dani wata irin azaba idan kika ce bakya tare da ni. Daga karshe ina miki fatan alkhairi, ina kuma sauraro daga gareki, nagode.
ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA MASU SAKA SHAUKI DA ƘARA ƘARFIN SOYAYYA.
Yabo da Jinjina Zai tabbata gareki ɗiyar kirki da aminchi, duk wata fata na Alkhairi Dole nai miki shi, kin zaburar da Zuciya Ta daga dogon suma na rashin irin ki a rayuwata, Zuciyata Ta Aminta Da Kalaman Ki Domin suna saka ni farin ciki, HubbyNa kece Abu mafi Ɗanɗanon Zaƙi mai canja tinani acikin rayuwata, tankaden DA nayi da kuma Reraya, Naga Ribar Shi Akan ki, HabibiNa Ina ƙaunar ki da Zuciyata da kuma Raina, Zan Cigaba da ƙaunar ki Har Zuwa Ranar Dana Daina Numfashi, Sahibata Ina Son Ki, Soyayyar ki ta rufe min idanu Bana Son Naji ko a Mafarki Labarin Soyayyar wata ɗiya Mace Sai naki HubbyNa, Samun ki Sa'a ce garen Babba Matata, Daga ƙarshe ina Fatan Sahibar Ruhina Tana cikin ƙoshin Lafiya. Sannan Ina Fatan kina Cikin Farin Ciki. Ina ƙaunar Ki.
❤❤❤
Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA
❤❤❤
Assalamu alaiki farin cikin zuciyata kuma sanyin idanuwa na, haƙiƙa kece mace ta farko wacce na yi gamo da ita karon farko, banta6a zato ko tsammanin za’ayi wata ƴa mace wacce zata sace min dukkanin ruhi a mafi ƙanƙantar lokaci ba sai ke, amma sai gashi ba tsammani nayi kicibus da kyakkyawar fuskar da na kasa ɗauke wa kallo, Haƙiƙa kyauwun ki yakai ayi misali dashi, kinsha gaban duk mai tinani, zuciyar ki Kyakkyawa ce, tafiyar ki mai tsari ne, Rayuwar ki abar kallo da koyi ce, lallai nayo matukar Sa'ar samun mace kamar ki a cikin rayuwata Muradina, Annuri na, Kuma Shalelen Zuciyata.
❤❤❤❤
Tambarin sarautar girma da ɗaukaka nake dokowa zuwa ga sarauniyata mai mulkin birnin zuciyata haƙaƙi kece gimbiyata wacce na damƙa farin ciki na da walwala ta a karkashin inuwar kulawarki.
Karanta: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA
Zanso ace nafi kowa matsayi a zuciyarki domin ina da yaƙinin nafi kowa ƙaunar ki shiyasa nace a kaf faɗin duniyar masoya babu tamkarki a fagen iya sarrafa zuciya da daddaɗan kalaman soyayya tabbas nayi dace da na kasance sarkin mulkin zuciyarki.
Ance so aljannar duniya ban fahimci hakaba sai da na kurbi zakin ɗanɗanon zumar soyayyarki sai kawai naji nayi suman zaune uhmmm ban ankara ba sai na tsinci kaina a sararin samaniya muna shawagi cikin duniyar masoya ina baki furennin lovayya.
bazanyi nadama ko dana sanin zaben ki da nayi a matsayin masoyiyata ba, saboda kece zuciyata ta zaba kece wacce raina ya aminta da ita, hakika burin zuciyata a gareki shine ki zama uwar ƴaƴana mukasance a tare har fitar nunmafashin mu.
Za6in Raina kike tilo, Bani kamar ki a zuciyata, tsananin ƙaunar da nake miki zuciyata ce kawai take iya ɗauka bakina kamantawa kawai yake, kina sani farin ciki, shigowarki cikin rayuwata Ya saitamin abubuwa da dama, Dani dake rabuwar mu sai Allah ba dai ɗan adam ba, babu wata ɗiya mace mai Zaƙin baki ko daɗin murya ko kyawun jiki kona fuska, iya tafiya ko kwarji da zata ɗaukemin hankali akan ki, Ke ɗin dai kece, kece Badaɗayata na faɗa Dake zanyi rayuwa bana son kowa sai ke. Idan muna da rai Zaki zamo matata, niko zan zamo miki miji, zamuyi rayuwa mai daɗi, zan debe miki kewa zan saka ki farin ciki iya iyawata, Zan Baki Duk Abunda Kike so.
Karanta: HANYOYIN-SAMUN-YADDAR-MACE
❤❤
HubbyNa Zan kasance dake ne a zuciyata Ba tare da wata fargaba ba, zan killace Soyayyar ki araina. Duk Ranar Da Nace Miki Bana sonki To Bani bane Sai dai wanina, Inason muyi zama na amana, mu baiwa junan mu yarda, kada musa raini a lamarin mu domin cigaban farin cikin mu muyi so dan Allah Na Gaskiya.
❤❤❤❤❤
Kyakkyawar zuciya tana rayuwa ne ƙarƙashin inuwar aminci,da amincewa, zuciyar da aka cudanyata da tsarkakekkiyar soyayya tana Samar da ingantacciyar lafiya agangar jikin mamallakinta, Haƙiƙa zuciya kalmace tamusanman don soyayya, soyayya kalmace ta musanmace don kulawa, ita kuma kulawa kalmace ta musanman domin ke, ke ta musanman ce agare ni... Ina yiwa Allah godiya daya bani nagarcecciyar mace irinki. My unforgettable.
Kada ku manta ku yi subscribe din wannan page din domin sanar daku da zarar mun dora sabon posting.
Muna Godiya da irin Gudummawan da kuke bamu. Muna tare daku iya wuya.
👉🏼Masoyan Wannan Shafi Ku abun Alfaharin mu ne a kullum, ku danna mana like👍🏻, Sambada na share🏃🏻♀🏃🏻♀. Sannan ku ajiye mana comment 🙏🏻 .
Ku kasance Tare Damu acikin wannan Shafin www.Qauna.com.ng
Post a Comment
Comment Section