KALAMAN SOYAYYA ZAFAFA

KALAMAN SOYAYYA ZAFAFA DOMIN MASOYA

Ku Mana Subscribe a Channel namu Dake YouTube👇🏻👇🏻👇🏻



A duk lokacin da Kika fada cikin kogin kewata, nikuma alokacin nake fadawa cikin tekun Tinanin ki. Bana iya kwashe Tsawon awanni Batare da na tina wacece ke acikin rayuwa ta ba. Bana iya Wuni guda ba tare dana ji sautin Muryarki ba. Koda yaushe naji wayata tayi kara tsammanin shigowar sakon ki nake mai cike da yabo daga wurin wacce tafi ko wace mace Sa'a acikin Zuciya ta. 
Ki tina cewa duk lokacin da kika fada kewata, Ina tare dake a fili da badini. Ina nan akusa dake. Nisa kawai kikai dani amma baga zuciyata ba. Bazan taba yin nisa dake ba Shalelena. 


Cikon Muradin Abinda Zuciyata Ta Qunsa Babu Kamar Soyayyarki Dake Ratsa Jinin Jiki Dare Da Rana, Sakamakon Ina Da Dalilin Kawar Da Duk Shakkar Samun Damar Mallakarki.


Sirrin Raena Shine Sadaukar Da Zuciya Da Gangar Jiki a Gareki Sarauniyar Asalin Girma Da Daukaka Acikin Rundunar Masoyan Duniya Domin Ina Dauke Da Alkawarin Zama Ma'abocin Farin Gani Lokacinda Nake Kallon Fuskarki.





Bani Da Qunci Ko Bakin Ciki a Yayinda Na Zamo Hijabin Kare Martabarki Daga Sharrin Magautan Da Basu Da Ra'ayi Akan Qaunar Da Muke Yiwa Juna. Shiyasa Nace Ba Makawa Inasonki.


Idan Na Zamo Adali Kece Ta Farkon Farin Samun Alkherin Da Nake Dauke Dashi, Shiyasa Kirari Da Yabona Ya Zamo Nishadinki a Dalilin So Da Qaunar da kike mu. Ina jin dadin kasancewa dake.




Tabbas furanni suna da qamshi, zuma kuma tana da zaqi, launin ciyawa kuma kore ne, amma ke babu wata kalma da zata iya bayyanar da zahirin siffarki sai dai kawai nace ke kyakkyawa ce, ina qaunar ki "my dear" ki sani cewa idan kika rabu dani zan shiga hadari soyayyar ki a cikin zuciya ta tamkar numfashi ne da yake futa daga hancina wanda tsayar dashi dai-dai yake da rasa rayuwa ta,  




Zan furta kalmar so a gareki a duk yanayin da nake ciki zan Ƙaunaceki a duk yanayin da kike ciki,
 ba zan guje kiba a duk tsanani ko wuya zan zauna dake koda a lambun qaya ne ina sanki son da bashi da abin kwatantawa, ina qaunar ki qaunar da babu wata y'a mace da zan iya mata koda kwatankwacin sane ina sonki so na gaskiya wanda ba yaudara aciki, bana son maqiyin ki koda kuwa ya kashe maqiyi na, 

  nakan ji komai ya wadatu gare ni idan nayi arba da kyakkyawan fuskar ki ki riqe ni tamkar yadda na riqe ki, ki sani cewa zanyi amfani da kyakkyawan fuskar ki domin ta zama adreshina 
Babu abinda zan iya 6oye miki tunda kin riga kin sani kuma kin fahimci cewa zuciyata ta riga ta jefa ni cikin tarkon da bazan iya ku6uta ba, kamar yadda na jima ina sanar dake cewa sansanin sonki kullum yalwa yake a cikin zuciya ta. 






Hkk kyakykywn sakone silar wanzuwar annurin dake cikin zuciyata awannan safiyar, amma kisani cewa turoshi garekine mahadin wadatuwar zuciyata da yarwa tacciyar ni' imar farinciki, domin isarda shi'agarekine yasa naturo miki sakome dauke da furucin sallama,  


Assalamu alaiki kyakykywr da zuciyata ke bugawa da haruffan sunanta, kamar yanda kikasani cewa daidaiton kowace gangar jiki ahadata da ruhinta to kahaka nima mahadin nawa farincikin shine, jin kyakykywr amsar da zatasanya annurin acikin zuciyata agareki, idan har yakinina zanto gaskiya agareki cewa kintashi lfy kamar yanda nima nata shi lfy, 



To zanka sance mematukar farinciki da shauki na mussan man, karbuwar sakona agareki shine karsashin da zuciyata zanta samu kamar yadda nakeji sanadin kaunarki wannan shine silar turomiki sakon barka da kyakykywr SAFIYA masoyiyata. 




Yake wacce tozalida kyakykywn murmushinta agareni yake zamowa silar kaisakon sanyaya ruhi gami da sanya dadda dan nayi azuci da gangar jikina, shinko kinsan kwangi lar aikin da zuciyata taibaiwa kwakwal wata silar wallafuwar kaunarki acikinta?, zuciyata tasa kwakwalwata natinani akan kyakykywr suffarki, amma nagama tunanina kaf bansamo sunan da zankira amatsayin nakiba, 





Domin suffarki sauyamin take tamkar wahainiya, hakanne yasa nakasa samun sunanki, matsatinki agareni bashida iyaka kinsa kosabo dame, hhmm sadin soyayyarki shine silar wanzuwar kaunarki azuciyata daddar muryarki itace zumar da kunwana kesan lasa, cikakkiyar kyakykywr surarki gami da takunki daidai shine abu mafi dadin hange aidanuwana, kyakykywr kwalliyarki kuwa ita idanuna ke farauta akowane lkc, 






Zankiraki da masoyiyata saboda kaunarki ce ma'abociyar rayiwar zuciyata, dalilin kiranki da abar kaunata kuma shine ruhina nasamun salamane idan natuna kewa kaunarki na zuciyata, da sunan kyakykyw zanyi maleji aduk lokacin da natuna asalin kyakykywr fuskarki azahiri, medadda dan saudi zankiraki sanadiyar tunawa da da dadan kalamanki cikin sanyin murya agareni, tsawon lokacin da kika dauka kina mulkar zuciyata ne zera nakiyaki da sauniyata. 




Aduk Lokacin da idanuwa na Suka kalli kyakkyawar Halittar ki, zuciyata ce take shiga wasi wasi. Jikina yakan faɗamin cewa wani sabon abu ya shigeshi. Shaukin ki dake shiga Zuciya ta yana son yafi ƙarfin zuciyata, sannan yana so ya zarce tinani na. Ban damu wacece ke ko a ina muka haɗu ba. Indai kece na yarda na kware miki. 

Kalamaina basu da ƙarfin da zan iya mallakar ZUCIYAR ki cikin sauƙi, amma nasan Zuciya ta zata ƙarfafa mini domin cigaba da nemo hanyar da zan Mallakeki





Linzamin Dake Jan Ra'ayina Shine Murmushinki
Akan Kyakkyawar Fuskarki Sakamakon Ina Da
Tabbacin Cewa Murmushinki Ne Silar Soyayyarki
a Fadar Xuciyata.

Zan Kare Martabarki a Lokacin Da Fushinki Zai
Bayyana Koda Zan Iya Zama Kurman Da Baya Ji
Da Gani Acikin Duniyar Nan.

Zan Dauke Dukkanin Sansanin Bakin Ciki Da
Rashin Walwala a Xuciyarki Matuqar Yin Hakan
Zai Zamo Nishadi Da Farin Ciki a Rayuwarki Ta
Duniya.






Hasken Qwayar Kyakkyawar Idaniyarki Shine
Sakon Da Kike Aiwatarwa Zuwa a Gareni Mai
Dauke Da Tabbacin Cewa Lallai Kina Sona.

Nayi Qudirin Daukar Damarar Samun Damar
Mallakar Makullin Xuciyarki Ta Hanyar Jan
Hankalin Masoya Da Kalaman So Da Qauna
Saboda Soyayyarki.

Yanayin Yadda Kalaman Bakinki Suke Fita Cikin
Salo Da Tattausar Murya Shine Yake Qara
Tunzura Zuciyata Akan So Da Qaunarki
Har'Abada.

Zan Kasance Adalin Cikakken Masoyi a Gareki
Matuqar Zaki Zamo Ma6oyar Sirri Da Alkawarin
Kasancewa Tare Dani Iya Wuya.

Fatana Akan Soyayyarki Shine Rokon Ubangiji
Mahalicci Da Ya Zamo Hijabin Kare Sharrin
Mahassada Da Magautah Dare Da Rana.






Kwalelen yan samari da kallon managarciyar fuskarki wadda take feso turaren farin ciki agareni shiyasa nake yawan ganinki har acikin mafarki


Lantarkin hasken dake haskake farin cikina yasamu asali daga tubalin tutar dake kadawa da tambarin fuskar rubutun sunanki

Alkawarin soyayyarki na daukarwa zuciyata komai zafin nisan tsanani da kunci zan kasance cikin biyayyar ladabi cikin duniyar kaunarki


Soyayyarki mai asalin samun asali ce wadda farkon asalinta yake faruwa acikin iskar danake shaka ina kaiwa zuciyata shiyasa nayi nisa cikin duniyar begenki

Akan sonki na shirya tsaf domin na sadaukar da jarumar zuciyata wajen yaki da masu nuna kiyayya agareki koda kuwa hakan zaisa narasa rayuwata sanadinki


Kin iya salo da takun iya kasaita kin zarce mata da yawa, Kallon kwalliyar fuskarki yazama abun koyi agaresu shiyasa suke kishi sanadin kin fisu zama kyakkyawar dake da halin mutanen kirki.

Banida burin kuntata miki napi kowa son kyautata miki 

Shiyasa zuciyata ta kara miki maki dan haka kar kiyi mamaki idan nace zuciyata na bar miki. Ina Sonki❤




Zanyi tafiya wacce bana wage ko waiwayawa domin tafiyace wacce yunwa da kishirwa domin tunanin gun wacce zani duk ya dauke mani zafin yunwa da kishiwar da ta addabi ruhina

Umarninki shine abunda zuciyata take tsumayin jira cikin kowanne lokaci da so da kaunarki nake yin numfashi

Bishiyar sonki tayi girman da tayi rassan da suke samar da sanyayayyar iskar da sanyin ta yake kara sanyayayya rai da ruhina

Assalama alaiki yake kworamar ruwan madarar da take maganiin dukkanin wata cuta wadda ta addabi zuciyata

Idaniyata ta makance ce ke kawai take da bukatar son gani a cikin kowacce safiya kece ta farkon ambatona hakan yasa nake kasancewar ciki farin ciki

Dominki nakeyin dukkanin wadannan zantukan ina fatana kina cikin yanayi na farin ciki tareda zumudin son ganin sakona wannan shine burin raina

A karshe ina maki fatan alkairi tare da fatan kasancewarki cikin irin yanayi na farin ciki da walwala da jindadi gamida annaahuwar da zata kara kusantar dake cikin yanayi na shaukin son ganina




Sautin Sarewar Amon Kalaman Bakinki Cikin Salo Da Tattausar Murya Shine Yake Kawo Famarki Izuwa Kunnuwana Har Nake Doka Tambarin So a Gareki Yake Nutsuwar Ruhina


A Zahiri Kece Mafificin Iskar Dake Samar Da Walwala a Tare Dani, Domin Kin Dauki Tutar Da Zan Iya Doka Miki Tambarin So Acikin Duniyar "Yammatah. 


Dadewar Sonki Acikin Zuciyata Ne Silar Saukar Kaunarki Aruhina, Kin Xamo Basarakiya Mai Girman Fada Sakamakon Ina Mai Qara Isar Da Jinjinar Girma Cikin Salama Yayinda Nake Doka Miki Tambarin So. 


Ina Muradi Da Dokin Kasancewa Ma'abocin Xama Sarkin Dake Mulkin Fadar Zuciyarki Sakamakon Kin Sadaukar Min Da Zuciyarki Daidai Lokacinda Nake Neman Tallafinki. 


 Yake Abar Sona Zanyi Alfahari Dake a Lokacinda Kowa Zai Bayyana Gwanarsa Acikin Ayarin Taron Masoyan Asali Domin Babu Wata Hanyar Da Mahassada Zasu Kai Farmanki Kushe Da Hassada Akan Fasalinki Na Kyawun Halittah. 


Alamunki Sune Suka Tabbatar Da Soyayyar Gaskiyace Tsakanina Dake Domin Babu Ranar Da Zan Kushe Halayyarki Cikin Suffofin Ma'abota Yaudarah Da Cin Zarafi.




Lallausar murya mai ratsa zuciya da kuma san yaya ruhi kin mallake zuciyata sarauniya ke daya ce tilo baki da tamka

A zahirin gaskiya ke kyakkyawace kuma.kina da zazzakar murya kamar anbusa sarewa

Wadda nake so kece domin da ke kadai zuciyata ta amince da ita bana jin san wata a cikin zuciyata sai naki sarauniyata ina sanki

Iya kyalliya mai ka,wata fuska sai sarauniyar kyawawa lawisa zanso na kasan ce dake na har abada

Sanyin muryarki ya zarce ko,rama wajan san yaya zuciya, adik lokacin da dare yayi ki da,ga kanki ki kalli sama zakiga wasu taurari masu matukar haske da sheki toh kema haka fuskarki take kasan cewa adik lokacin da kika yi murmushi


A gaskiya ke kar,she ce wajan iya kalamai masu ratsa zuciya gaki da fararen idanuwa masu haske 




Post a Comment

Comment Section

Previous Post Next Post